Yadda zaka duba Neco Results dinka cikin sauki

Barka Da Zuwa labaranhausa.com A Yau Insha Allahu Zamu Nuna Muku Yadda Ake Duba Neco Result Na 2021,

Dalilin Dayasa Muka Kawo Muku Yadda Ake Duba Neco Result Shine Saboda Mutane Da Dama Suna Tambayarmu Ta Wace Hanya Ake Duba Neco.

Hanyoyin Da Ake Duba Neco Result Sun Kasu Gida Biyune

My NECO RESULT 2000 – 2018 Wannan Itace Tsohuwar Hanyar Da Ake Duba Neco Result Wadda Idan Mutum Ya Duba Zai Ga Daga Iya Shekarar Dubu Biyu Da Sha Takwas 2018 Ta Tsaya.

NECO Result 2000 – 2021 Wannan Itace Sabuwar Hanyar Da Ake Duba Neco Result Wadda Idan Mutum Ya Dubu Zai Ga Daga Iya Shekarar Dubu Biyu Da Ashirin Da Daya 2021 Ta Tsaya.

Yadda Ake Duba Neco Result
Step 1:- Abu Na Farko Da Zaka Farayi Shine Zaka Shiga Wannan Link Https://Result.Neco.Gov.Ng/ Zai Bude Maka Wani Shafin Kamar Haka:

Step 2:- Abu Na Biyu Da Zaka Karayi Bayan Yabude Maka Shafin Zai Baka Damar Kasaka Shekarar Da Akayi Jarrabawar Necon Wato (Exam Year).

Step 3:- Abu Na Uku Da Zaka Karayi Shine Da Akwai Inda Aka Saka (Exam Type) Idan SSCE Internal JUN/JULY Ce Saika Saka Idan Kuma SSCE External NOV/DEC.

Step 4:- Abu Na Hudu Shine Saika Saka Token Din Da Kasiyo Wato PIN Kenan Saboda Shine Zai Baka Damar Da Zaka Iya Ganin Jarrabawar Ta Neco.

Step 5:- Abu Na Biyar Shine Da Akwai Inda Aka Saka Registration Number Saika Saka Registration Number Dinka Ta Neco Din Bayanka Saka Daga Kasa Da Akwai Inda Aka Rubuta Check Result Saika Danna Shi Kana Dannawa Sakamakon Jarrabawarka Zai Bude

0
0

Labaran Hausa

Labaran Hausa: Kafar Sadarwa ce wadda zata dinga kawo muku bayanai dangane da al'amura da suke faruwa a gidan Nijeriya, Afrika dama Duniya baki daya. Tabbatar da ka danna subscribe bottum dan samun damar dinga sanar da kai a duk sanda muka dora sabon Labarin mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *