Yadda aka gudanar da jana’izar Kwamishinan da yan Ta addan suka kashe a jahar katsina
An kai marigayi kwamishanan Kimiya da Fasaha na jihar Katsina makwancinsa Manyan Malamai da jagororn siyasan tarayya da jihar Katsina sun halarci taron jana’izar
An gudanar da addu’o’in Allah ya jikansa kuma ya karbi shahadarsa An binne marigayin ne a makabartan Gidan Dawa bayan Sallar Jana’izar,
Rahoto DailyTrust. Wasu suka hallaka marigayin ranar Laraba cikin gidansa. Wadanda suka halarci Jana’izar sun hada da Gwamnan jihar Katsina,
Aminu Bello MAsari da tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin mai bada shawara kan lamuran tsaro, Manjo Janar Babagna Monguno.
Sauran sune Sifeto Janar na yan sanda, Usman Alkali Baba; Shugaban hukumar DSS, Yusuf Magaji Nasir; Shugaban hukumar NIA, Ahmed Rufa’I Abubakar da MAnjo Janar Samuel Adebayo.
Allah ya jikan sa da rahama kamar yadda kukaji wannan kwamishinan har gida aka bishi aka kashe shi Allah ya karbi shahadar sa Allah yasan chan yafimar nan muna godiya da ziyara.