Tir da wannan badalar, wai ace musulmi ne zasu aikata wannan tir…
A yanzu nan majiryarmu ta samu wani labari mai ban takaici da al’ajabi da ban dariya duba da irin yadda kowa yake ta cikinsa amma su wai karanci kuɗin fata kuke kuka kamar yadda jaridar Daily Nigerian Hausa na ruwaito.
Wasu karuwai a babban birnin tarayya, FCT, Abuja sun koka kan rashin ciniki a kasuwancinsu sakamakon karancin tsabar kuɗi a hannun kwastomomi.
Sun ce duk da cewa manufar musanya kudi abin yabawa ne, amma yadda ake aiwatar da ita a halin yanzu kalubale ne ga kasuwancinsu.
Karuwan sun ce abokan cinikin su sun ragu sosai saboda halin da ake ciki na rashin tsabar kuɗi.
Sun bayyana yanayin a matsayin abin takaici da tafiyar hawainiya ga kasuwancin su.