Shiga ka gani Hukumar Hisbah ta kama maza masu yunkurin auren Jinsi A kano, InnaLILLAHI wa Inna Ilaihi Rajiun…

Hasbun Allahu wa ni’imal wakil, ga wata musiba ta tinkare mu ya Allah Kayi mana maganin ta ta kafin tazo tafi karfin mu, Ameen ya Hayyu ya Qayyuhm, Da ji muke ana irin wannan abin amma yanzu

a cikin Garuruwan mu ake yunkurin farawa, Allah ka tsare mu, Allah Yasa kuma wannan Shine na karshe a Kasar mu, Ameen. Hukumar Hisba Sun samu Sanarwa ana yunkuri hada auren jinsi wato

Auren Namiji da namiji a Jahar kano tayi maza maza taje ta dakatar da abin ta kama mutane goma sha tara (19) Wadanda a cikin su akwai mata goma sha Biyar (15) da kuma maza su su Hudu (4)

Masu auren sun samu nasarar tserewa Amma an kama mutum 19 daga cikin wadanda suka halarci filin taron auren, Ubangiji Allah ya sa mu dace, Jaridar HAUSALEGIT Ta rawaito wannan Labarin.

0
1

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *