Miji Ya Dawo Gida Ya Kama Matarshi Da Likinta Dake Duba Lafiyarta Turmi Da Tabayar Suna Aikata Lalata

Wani magidanci wanda ya dauki tsawon shekaru da matarshi daya tilo sannan Allah bai basu haihuwa ba. Ya dawo gidan ya kama matarshi da likinta dake duba lafiyarta turmi da tabayar suna aikata lalata.

Wannan miji ya bayayya irin yadda yaji a wannan lokacin yace “A rayuwar shi bai taba tunanin matarshi zata iya tsayawa daidai da minti daya tayi tunanin cin amanar shiba bare kuma ta aikata domin yana ganin ya rike mata amana Ya hakuri da yara saboda farin cikinta saboda itace wacce bata haihuwa.

Yaki kara aure saboda bayason ya ganta a cikin irin damuwar da zata shiga idan wata tazo ta haihu, ci da sha da sutura mai kyau daidai da minti daya bai taba gajiyawa ba ko tunanin wani yaro kawai burina shine na ganta cikin farin ciki.”

Bayan wannan hira da akayi dashi matar ta bayyana dalilinta na amincewa ta aikata wannan mummunan aiki tare da likita ta fara da cewa “Wannan likita miji nane ya dauke shi aiki kawai saboda ni domin matsalar da nike fama da ita ta rashin haihuwa dalilin shine akwai wani kitse dake a jikin mahaifa ta.

Wanda shine yake hana na kamu da ciki sannan kuma likitan ya bayyana ko anyi aiki ma saidai a karasa lalata mahaifar dukka amma saidai ya ce akwai wani wasu alkurori dazai dinga zuwa gida yana min zasu kona wannan kitse amma sai anyi hakuri domin za’a dan dauki lokaci ni da mijina muka amince.

Wannan likita ya cigaba da zuwa a ranar da wannan abu zai faru tsakanina dashi yace min ne zai fadamin wata gaskiya da ake boyemin nace ina jin sai yake fadamin ai wannan matsalar rashin haihuwar ba daga ita bane daga mijinta ne kawai ya boye ne saboda ya lura yana son haihuwa sosai.

A lokacin da ya fadamin wannan magana naji haushi matuka har ina cewa shine wanda ya cuce ni ba mijina ba sai yake cemin idan kina so zaki iya haifarwa mijinki yaro nikuma ina matukar son naga mijina a cikin farin ciki kamar yadda yake son ganina.

Saina amince nace masa taya sai yace shine wanda zai sakamin cikin dashi zan kwanta sau daya yana da ilimin da ciki zai shige ni ba tare da kuma an gane wannan yaro ba yaron mijina bane a yanayin da nagani na likitan ya nunamin da gaske son taimako na yake bawai yana son amfani dani Bane.

Bayan na amince yace zan biya shi kudin aiki ya fadamin kudi nayi masa taransifa. Muka shiga daki muna farawa sai ga mijina ya dawo ya ganmu da idonsa muna aikata wannan abu a lokacin nan nasan zamanmu ya kare tare dashi domin koda ya bani damar yi masa bayani bazai yarda da abinda zance ba.”

Wannan shine abinda ya faru yanzu haka wannan miji ya sake ta daga baya kuma ta gano wannan likita ya yaudare ta ne dama son amfani yake da ita.

0
0

Labaran Hausa

Labaran Hausa: Kafar Sadarwa ce wadda zata dinga kawo muku bayanai dangane da al'amura da suke faruwa a gidan Nijeriya, Afrika dama Duniya baki daya. Tabbatar da ka danna subscribe bottum dan samun damar dinga sanar da kai a duk sanda muka dora sabon Labarin mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *