Karo nafarko Datti assalafiy yayi fata fata da shugaban kasa Muhammadu Buhari kunsan asirin da ya tona masa kuwa

Datti assalafiy ya tura sako mai zafi akan shugaban cin Muhammadu Buhari da kuma masu shirin fita zanga zanga zanso kuji mai Datti assalafiy ya fada akan wannan rubutun nasa gashi nan.

Tun jiya ake shiri a wasu jihohin Arewacin Nigeria, yau za’a fara fitowa zanga-zanga domin bayyana bakin ciki da damuwa akan matsalolin tsaro da ya addabi Arewa ba tare da Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dauki matakin da ya dace ba

Ni Datti Assalafiy sakona gareku masu shirin fara fita zanga-zanga, ku sani cewa dokar kasa ta baku wannan damar matukar zanga-zangar lumana ne

A wani labarin na da ban Tsohon mijin mome gwambe Adam fasaha zai auri Nana ta cikin shirin izzar so 👇👇👇

Amma ina baku shawara kar a bar wani ya dauki makami, kar a kyale kowa ya taba kayan wani ko kayan Gwamnati
Mu sani cewa Nigeria tana kan tsini, ana neman duk wata hanya da za’a haddasa mummunan yaki a Nigeria, amma hakan ba zai faru ba sai idan ‘yan Arewa sun bada hadin kai

Wadannan miyagun ‘yan siyasa makaryata mayaudara da muke gani, sun tara kudin haram, sun saita hanya, a shirye suke da zaran wutar yaki ya kunnu a Nigeria su kwashe matansu da ‘ya’yansu da karuwansu su tsere daga Kasar a barmu cikin wahala muna konar kasarmu

A karon farko na goyi bayan a fita zanga-zanga domin a ladabtar da Gwamnatin Baba Buhari, amma a kula sosai banda ketare iyaka, mu aza kishin kasarmu da yankin mu a gaba
Allah Ya taimakemu

0
0

Labaran Hausa

Labaran Hausa: Kafar Sadarwa ce wadda zata dinga kawo muku bayanai dangane da al'amura da suke faruwa a gidan Nijeriya, Afrika dama Duniya baki daya. Tabbatar da ka danna subscribe bottum dan samun damar dinga sanar da kai a duk sanda muka dora sabon Labarin mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *