Kai kai Shiga ku kalli abinda baku taba ganin irin shi ba a addini, se ku fadi fahimtar ku a kai a ilimance a kan wannan abin…

Rayuwa kenan kullum abubuwan se kara bullowa suke tayi, a tarihin Addinin mu dai bamu tabajin an wakilci mace da ta ja ragamar Sallah Ba, amma se gashi a cikin Bidiyon nan muna ganin

wata baiwar Allah Mai suna Imamah Jamila tana Jan Mutane Sallah Daga a Sahun nasu a kwai mata da maza, a kaf cikin Al Kurani da sunnar Manzon Allah (S.A.W) ban taba jin inda aka ce mace taja Sallah ba

kai ban ma Ga inda akace mata su shiga masallaci suyi Sallah tare da maza ba Sai Maryam Yar Imrana mahaifiya ga Annabi Isah (Allah Ya Kara musu yarda).

Amma A Fahimtata Zata Iya Jan su sallah idan har ya kasance Ita kadaice mahaddaciyar Al Kurani a cikin su kuma babu namijin da ya san dokokin sallah a cikin su da kuma haddar al Kurani koda na akalla hizfi daya ne, wato maana ya kasance basu jima da karbar Addini ba kuma babu namiji mai ilimin Addini

a kusa dasu wanda zai zo ya koya musu, toh a wannan halin ya zama Fardu Ayn (Farillan Aynihi) kenan Wato ya zama dole a kanta ta koyar dasu yadda zasu gudanar da Addinin su da kyau,

Allahu Aalam Allah shine masani, Idan munyi daidai Allah ya karba mana idan kuma munyi kuskure Allah ya gafarta mana, Ameen ya Hayyu ya Qayyuhm ya Dhuljalal wa al Ikram.

0
0

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *