Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: yaune Allah ya yiwa Sheikh Ahmad Bamba Kala Haddasana rasuwa wanda kukafi sani da Ahmad BUK

Innalillahi wa inna ilaihim raji’un
Allahu Akbar Duniya labari: yanzu yanzu muka sami labarin mutuwar ficaccan malamin addinin Musulinci dake Jihar Kano Sheikh Ahmad Bamba Kala Haddasana.

Sheikh Ahmad Bamba Kala Haddasanaya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi, kuma ya rasu ne a Asibitin koyarwa ta Malam Aminu Kano.

Iyalan Malamin sun sanar da cewa za a yi jana’izar malamin a Masallacin Darul Hadis da ke unguwar Tudun Yola a birnin Kano bayan Sallar Juma’a.

Duk masu bibiyar wannan malamin sun san yayi fice a wajan karatun hadisi wanda yake karan tarwa acikin masallacin BUK sai dai daga baya ya bude nasa mai suna “Darul hadis”

0
0

Labaran Hausa

Labaran Hausa: Kafar Sadarwa ce wadda zata dinga kawo muku bayanai dangane da al'amura da suke faruwa a gidan Nijeriya, Afrika dama Duniya baki daya. Tabbatar da ka danna subscribe bottum dan samun damar dinga sanar da kai a duk sanda muka dora sabon Labarin mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *