Hadiza gabon ta saki wani zazzafan sako na tonawa manyan arewa asiri Adai na zagin Dr isa ali fantami akan harkar tsaro
“Allah Ka Saka Wa ‘Yan Arewa, Ana Ta Kashe Su An Rasa Mai Magana”. Inji Hadiza Gabon fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood Hadiza Aliyu Gabon,
Ta nuna ɓacin ranta a fili game da yawan kashe-kashe da ake yi a Najeriya, musamman anan yankin Arewa kamar yadda akai wani nan bada jimawa ba kuma aka kone mutanan.
Jarumar dai ta wallafa wani gajeren saƙo da ta rubuta a shafinta na facebook jarumar ta yi Allah ya isa kan wannan kashe-kashe da ake yi wa yankin Arewa, kuma babu mai iya tsawatarwa.
Hadiza Aliyu wacca kukafi sanin da Hadiza Gabon ta bayyana cewa, “Yaro ɗaya aka kashe a Lagos an fita nemar masa haƙƙinsa, ba maganar jam’iyya ko addini ko jinsi,
Amma mu anan ana ta kashemu an rasa masu magana, Allah ya saka mana”. Kashe-kashen da akai na baya bayan nan dai, shi ne na wasu matafiya kusan aƙalla 40
Da yan bindiga suka cinnawa wuta a cikin mota, suka ƙone su ƙurmus. awani labarin na daban
Mene Ne Laifin Minista Sheik Pantami Game Da Kashe-Kashen Da Ake Yi A Yankunan Arewa?

Na ga dai shi ba ministan tsaro bane, ba mai bada shawara kan harkar tsaro bane, amma ban san me ya sa da zarar an samu baraka kan harkar tsaro a kasar nan, sai a dinga tsoma shi cikin masu alhaki a sha’anin tsaron Nijeriya.
Daga Jeeddat Sa’idu