Haba jama’a wannan ai kwartanci ne ba kwamedi ba Idan baka da aure karka shiga akwai matsala…

Anyi Kira ga Hukumar Hisbah Tasa ido Akan irin Abubuwan da Abdul Bubulaye Yakeyi Wanda Sun Sabawa Al’ada da Addini, Haba jama’a wannan ai kwartanci ne ba kwamedi ba Idan baka da aure karka shiga akwai matsala.

Mutane da dama Sunyi kira ga Hukumar Hisba akan ta kira jarumin barkwanci watau Abdul babulaye Wanda ke sakin bidiyon barkwanci hade dana batsa a kafafen sada zumunta na zamani.

Matashinnan wanda yayi ƙaurin suna wajen sakin bidiyon barkwanci wani lokacin hadda na batsa mai suna Abdul Babulaye ya fitar da wani bidiyon da bai dace ba.

Ana zarginsa da yin kalamai na banza waɗanɗa basu dace ba, a koyarwar addinin Musulunci dama al’adar malam bahaushe.

Dama dai tuni ake kiraye kirayen cewa ya kamata a taka masa burki kan irin abubuwan da yake yi a shafukan yanar gizo. Domin abun nashi kullum gaba gaba yake karawa Yanzu takaiga harda matarsa ta sunna daya aura yake sawa a Shafukan Sada Zumunta sunayin abubuwan da basu dace ba.

Mun gode da Ziyartar wannan Shafi namu wanda yake kawo maku labarai da dumi duminsu Mungode

Daga AREWADROP.COM

0
0

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *