Dan Allah ku duba yadda ake nuna jimami mutun daya aka kashe amma kalli abun yake faruwa

RAN MUTUM DAYA a ka kashe a America amma sai da a ka dauki tsawon lokaci a na lallashin mutanen da ke zanga zanga, hatta jami’an tsaron kasar sai da su ka durkusawa masu zanga zanga don nuna alamar ba da hakuri, ba su bugi kowa ko tafiya da wani ba

Idan mun san ba za mu iya kwaikwayon salon mulkinsu ba kamata ya yi mu ajiye tsarin mulkin demokoradiyya mu dauki kama-karyar da mu ka fi iyawa,

amma ba daidai ba ne shugaba ya rantse idan ya karbi mulki zai kare kasa da rayukan mutanen kasar da jin dadinsu kuma ya kasa, sannan a ce ba za a yi magana ba

Hujjar da a ke kafawa kasar ta na a kan tsini bai kamata a yi adawa ko zanga zanga ba wa ya kai kasar kan tsinin? Tunda gwamnatin nan ta karbi mulki mutane su ke wash ! Don me kasa ba za ta hau kan tsini ba?

Wata hujjar kuma sai a ce ai yan adawa ke daukar nauyin ta’addancin su ke daukar nauyin komai. Idan an san wadanda ke daukar nauyin ta’addanci a kama su ma na a hukunta su.

Ni ban yarda wasu sun fi karfin gwamnati ba, idan ni ke rike da kasa cikin biyu dole a yi daya, ko dai in murkushe masu kutunguila in ga bayansu, ko kuma su murkushe ni ina kan mulki su ga bayana

Don haka duk wadanda su ke ganin a tafi a haka a lallaba ana sadaukar da rayukan talakawa don kada gwamnati ta watse shine daidai, yakamata su kalli hoton yadda za su ji idan….

A ka kwantar da mahaifiyarsu ko kanwarsu a ka yi mata fyade a kan idonsu a ka kashe ta bayan an gama yi mata fyaden, ko kuma idan matarsu ko yayansu ke a cikin mota a ka bankawa motar wuta su ka kone kurmus

Lokaci ya yi da za mu koyi tare jifa ko da ba a kanmu za ta fada ba.

0
0

Labaran Hausa

Labaran Hausa: Kafar Sadarwa ce wadda zata dinga kawo muku bayanai dangane da al'amura da suke faruwa a gidan Nijeriya, Afrika dama Duniya baki daya. Tabbatar da ka danna subscribe bottum dan samun damar dinga sanar da kai a duk sanda muka dora sabon Labarin mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *