Babbar magana Wane irin abin kunya ne wannan, ace An kama ka ka saci kudin sadaki…

toh fa ana wata se ga wata Wai ace An Sace Kudin sadaki a gurin daurin aure wannan ba karamin abin mamaki bane gaskiya, ya Allah Ya Shiryi dukkan mai irin wannan tunanin

kamar yadda muka samu Labarin cewa a ranar asabar da ta gabata wannan abin ya faru a unguwar Fagge quartet da ke karamar hukumar Tarauni, A nan cibiyar kasuwancin arewa wato Kano.

Angon da ya Nemi a sakaya sunan sa ya bayyana cewa ana daf da za a daura auren nasa aka sace masa Kayan sa da yasha wahala ya tara kudi ya dinka kuma ya samesu sama da kasa bai gani ba

kuma ana cikin daurin auren nasa aka yi wuff da kudaden sadakin nasa, Allah Sarki bawan Allah ya Jarabtu, Toh Fatan mu Shine Ubangiji Allah Ya Shiryar damu baki daya, don wani ma ba barawo bane

amma a hakan yake satan ba don  yana so ba, saboda halin da ake ciki, saboda haka banda tsinuwa ko zagi domin masu iya magana sunce da Rigimar ciki kwara ta waje. Allah Ya sa mu dace. Ameen.

0
0

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *