Babbar magana ko kai ka kalli wannan abin da ya faru bazaka so ace yar uwarka tana film ba…

Matashiyar jarumar kannywood wato Amal Umar tayi wata magana wacce a zahirin gaskiya da yawa wasu daga cikin yan kannywood basuji dadi ba domin kamar cin fuska ne amma ita kuma tayi ne domin a kullum butinsu shine su kawo gyara a wannan ma’aikata ta yadda zata samu cigaba.

Ta bayyana haka ne a wata sabuwar hira da gidan jaridar BBC Hausa sukayi da ita wanda wannan jarumar ta dinga fadar wasu matsaltsalu wanda kannywood take fuskanta yanzu musamman daga wajen jama’ar gari sabuwa da irin kallon da ake musu na rashin fahimta.
 
Ta fadi maganganu da dama wanda idan aka tsayi aka dubesu da idon basira za’a Tabbatar da abinda wannan jarumar ta fada tunda yanzu an mayar da kannywood kamar wata majillisa ta marassa kunya bayan kuma sune wanda al Ummu suke kallo domin kwaikwayon wasu halaye nagari daga garesu shine yasa tayi wannan tufkar domin a daure a kawo gyara a wannan masana’anta mai albarka wato kannywood.

0
0

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *