Ana wata sai ga wata Wani babban Director yasa hukuma ta kama Jarumi sadik sani sadik Takarfi wannan bidiyan sai ya baku mamaki…

Kotun shari’a da ke unguwar Hotoro masallacin juma’a a birnin Kano zata saurari karar da aka shigar kan Jarumin masana’antar Kannywood,

Sadiq Sani Saniq bisa zargin yin ruf da ciki kan kudaden wani bawan allah, aliyu muhammad hanas wanda darakta ne kuma furodusa a masana antar shirya fina finan hausa.

Ya shigar da korafin jarumi Sadiq Sani Saniq kan cewa, yana bin sa kudade amma jarumin ya ki ya biya shi ya kuma yi masa alkawari fiye da shurin masaki bai biya ba, karshe ma sai ya daina daukan wayarsa.

Na tuntubi Gambo (Sadiq Sani Sadiq) kan wani fim da nake so ya fito min a ciki mun yi ciniki da shi na dakko kudi na ba shi, sai aka sami matsala bai zo ba na daga lokacin aikin nan ma bai zo ba.

Karshe dai na nemi Ali Nuhu ya maye min gurbinsa daga baya ne na nemi ya dawo min da kudina amma sai ya yi ta min wasa da hankali, cewar Furodusa Aliyu Hanas.

Ya kara da cewa: Akwai sanda na sami labarin yana cikin, shoprite Kano na dauki ‘Yan Sanda muka tafi don hukuma ta tirsasa shi ya ba ni hakkina,

A lokacin ne ya ba ni wani abu daga kudin ta hannun Maje Elhajeej Hotoro,
Furodusa Usman Muazu ya yi kokarin shawo kan sa ba shi ka dai ba har da su Alasan Kwalle da su Sulaiman Abubakar

Amma bai ba ni kudina ba, don haka na maka shi a Kotudon a yi mana shari’a ya dawo min da hakki na, cewar Darakta Aliyu Hanas.

0
1

Labaran Hausa

Labaran Hausa: Kafar Sadarwa ce wadda zata dinga kawo muku bayanai dangane da al'amura da suke faruwa a gidan Nijeriya, Afrika dama Duniya baki daya. Tabbatar da ka danna subscribe bottum dan samun damar dinga sanar da kai a duk sanda muka dora sabon Labarin mu.

One thought on “Ana wata sai ga wata Wani babban Director yasa hukuma ta kama Jarumi sadik sani sadik Takarfi wannan bidiyan sai ya baku mamaki…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *